Yanzu-Yanzu: Shugaban Kasar Lebanon Ya sauka daga Mulki.
Gwamnatin Lebanon ta sauka daga mulki a yayin da 'yan kasar ke ci gaba da nuna fushinsu sakamakon fashewar wasu abubuwa ranar Talata a tashar jirgin Beirut lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 200.
Firaiministan kasar Hassan Diab ne ya bayyana haka ta gidan talbijin ranar Litinin da yammaci.
Mutane da dama sun dora alhakin fashewar kan cin hancin da ke faruwa a cikin gwamnati.
Masu zanga-zanga sun kwashe kwana uku suna gangami a kan tituna inda suka rika arangama da 'yan sanda.
An samu fashewar ne sakamakon bindigar ton 2,750 na sinadarin ammonium nitrate wanda aka adana a wuri maras tsaro cikin shekaru da dama.
"Yau mun bi umarnin jama'a da bukatarsu ta hukunta wadanda ke da alhakin aukuwar wannan masifa wadanda kuma suka kasance a boye tsawon shekara bakwai, da kuma bukatar jama'a ta samun sauyi na hakika," in ji Mr Diab.
Shugaba Michel Aoun ya amince gwamnatin ta ci gaba da aiki a matakin wucvin gadi har lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati.
No comments:
Post a Comment