Zidane zai jagoranci kungiyar Real Madrid a kakar wasa mai zuwa - Mahanga

Barka da zuwa shafin mahanga, Mahanga shafi ne da zai dinga kawo muku labari masu banmamaki da ban dariya , tare da littatafai na hausa wato ( novel's )

People Online

Breaking

ads

Thursday, 23 July 2020

Zidane zai jagoranci kungiyar Real Madrid a kakar wasa mai zuwa

Shugaban kungiyar Real Madrid Florentino Perez ya tattauna da manajan kungiyar Zinedine Zidane a karshen wannan kakar, kuma sun amince tsohon dan wasan faransan zai cigaba da jagorantar kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

Zidane ya kasance tsohon dan wasan Real Madrid kuma yayi ritaya a kungiyar bayan yanada sauran shekara daya a kwantirakin shi. Amma ya dawo kungiyar a shekara ta 2018 a matsayin kochi wanda har yayi nasarar lashe kofin gasar La Laga. Yanzu shekaru biyu ne suka rage a kwantirakin Zidane.




A kakar wasan bara Zidane ya bayyana cewa yana so ya lashe kofin gasar kuma yanzu hakan ya tabbata. Florentino Perez ya fadi cewa Zidane kyauta ce ga kungiyar Real Madrid bayan Ramos ya daga kofin gasar a ranar alhamis din data gabata.

Kungiyar Manchester City da Real Betis sun ba tawagar Zidane kashi a wannan kakar kafin aje hutun korona, amma yanzu kuma bayan an dawo daga hutun tawagar ta dawo da kuzari sosai wanda har yasa suka lashe kofin gasar La Liga sauran Champions lig

No comments:

Post a Comment

ads1