TARIHIN TAJ MAHAL - Mahanga

Barka da zuwa shafin mahanga, Mahanga shafi ne da zai dinga kawo muku labari masu banmamaki da ban dariya , tare da littatafai na hausa wato ( novel's )

People Online

Breaking

ads

Friday, 12 February 2021

TARIHIN TAJ MAHAL

 AL'AJABI: Takaitaccen Tarihin Ginin Taj Mahal

Taj Mahal daya ne daga cikin abubuwan al'ajabi bakwai da ake da su yanzu haka a duniya. Shi dai wannan gini na Taj Mahal tarihi ya bayyana cewa wani kabari ne da sarki Shah Jahan ya sa aka ginawa matarsa ta uku mai suna Mumtaz Mahal domin tunawa da ita a matsayinta na wacce ya fi so da kauna a rayuwarsa. Wannan kasaitaccen gini na Taj Mahal yana yankin Agra ne ta kasar Indiya, kuma an bayyana cewa shi ne kyautar SOYAYYA mafi tsada a duniya, ginin yana da tsawon mita 73 (daidai da kafa 240) Ustad Ahmad Lahauri shi ne ya zana taswirar ginin.

Sarauniya Mumtaz Mahal ta rasa ranta ne lokacin da ta zo haihuwa ta goma sha hudu. Mutuwarta ya girgiza Sarki Shah Jahan matukar girgizawa inda yasha alwashin yi mata kyautar da za'a rinka tunawa da ita har duniya ta tashi.



Hakan kuma aka yi sarki Shah Jahan ya tura sassa daban daban na duniya aka nemo masa kwararrrun magina sama da dubu ashirin (20,000) suka kama aiki dare da rana domin wannan gini na Taj Mahal. An fara ginin ne a shekarar 1632; aka kuma kammala a shekarar 1653. Kimanin shekaru ashirin da biyu (22) ke nan ana aikin. A wancan lokacin ginin ya ci kimanin rufi'in Indiya har milyan 32, wanda darajarsu a yanzu sun kai Rufi'i bilyan 52.8, (daidai da dalar Amurka milyan 827).

Bayan an kammala ginin a shekarar 1653, sai Sarki Shah Jahan ya sa aka tara kwararrun maginan da suka yi aikin tare da ba da umurnin datse hannayen su. Dalilansa na wannan danyen aiki shi ne don kar su je su sake gina wani makamancinsa a wani wuri.

A yau an wayi gari ginin Taj mahal mai shekaru dari uku da tamanin da uku (383) shi ne gini tilo da babu makamancinsa a duk fadin duniya wajen tsari da daukar hankali. A halin yanzu gawar Shah Jahan da na matarsa Mumtaz Mahal na rufe a cikin wannan katafaren ginin da ya zamo tamkar sansanin 'yan yawon bude ido daga sassa daban daban na duniya (kimanin mutane milyan uku suka ziyarci ginin a shekarar 2003).

Babban jagoran ginin wanda shi ma aka datse

No comments:

Post a Comment

ads1