Bayan Watanni 4 da Aure: “Limamin Wuf ya rabu da Wuf dinsa - Mahanga

Barka da zuwa shafin mahanga, Mahanga shafi ne da zai dinga kawo muku labari masu banmamaki da ban dariya , tare da littatafai na hausa wato ( novel's )

People Online

Breaking

ads

Monday, 10 August 2020

Bayan Watanni 4 da Aure: “Limamin Wuf ya rabu da Wuf dinsa

 Bayan Watanni 4 da Aure: “Limamin Wuf ya rabu da Wuf dinsa”

Tauraron fim din Kwana Chasa’in da tara na gidan talabijin din Arewa24, Abdul Sahir wanda ya fito da salon Wuf inda ya auri tsohuwar ‘yar takarar sanata a jihar Kaduna, Hajiya Bilkisu Shibah, Rahotanni sun bayyana cewa Auren nasu ya mutu.

A lokacin aurensu lamarin ya dauki hankula sosai inda akai ta bayyana ra’ayoyi mabanbanta wasu da dama sun yaba wasu kuma sun bayyana kasin haka.



A watan Afrilune dai maganar auren su ta bayyana ga Duniya inda lamarin ya dauki hankula saboda Amaryar ta girmeshi. Saidai ya bayyanawa Mujallar fim a wancan lokacin cewa bai damu ba.


 



Rahoton da muka samu daga Rariya ya bayyana cewa auren nasu ya mutu. Watanni 4 kenan bayan da aka yishi.




 


Hakanan duba shafin Instagram na Abdul Sahir ya bayyana cewa ya cire hotunan matar tasa daga shafinshi inda a baya hotuna da bidiyonsu tare suka cika shafin nashi.



Da dama dai nata mai tambaya kan lamarin amma bai bayar da amsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.


No comments:

Post a Comment

ads1