Hotunan Mawakin da Kotu ta yankewa Hukuncin Kisa bayan samunshi da cin zarafin Annabi(SAW) a Kano
Wannan hotunan matashinnan me shekaru 22, Yahaya Aminu Sharifai kenan da Kotun Musulunci a Kano ta yankewa hukuncin kisa bayan samunshi da laifin kalaman batanci ga fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad(SAW).
Hakanan kotun ta daure wani Umar Farouk Sharada tsawon shekaru 10 saboda kalaman da basu kamata ba ga Allah yayin gaddama.
Bayan cin zarafin da Matashin ya aikata na fiyayyen Halitta, Fusatattun matasa sun rushe gidansu inda kuma aka yi tattaki zuwa Ofishin Hisba dan neman a dauki mataki akansa.
No comments:
Post a Comment