
Ba zamu kara gayyatarshi ya bayyana a gaban mu ba>>Kakakin Majalisa, Gbajabiamila ya fada akan shugaban NDDC da ya suma
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa kwamitin majalisar ba zai zake gayyatar shugaban NDDC da ya Suma a gabansu lokacin ana bincikarshi ba.
Femi ya bayyana hakane bayan da kwamitin ya dawo ya ci gaba da zaman binciken bayan hutun da ya tafi sanadiyyar suman shugaban NDDC, Kemebradikumo Pondei.
Yace daga yanzu wasika zasu rika aike masa. Yace yana mai fatan Allah ya sauwake sannan kuma ya aika likitan Majalisar ya je ya dubashi.
Daga nan ya mukawa kwamitin majalisar ci gaba da binciken
Ajiye ra,ayinka dangane da labaranmu shawara ko kuma korafi mugode

No comments:
Post a Comment