
Shugaban kwamitin majalisa dake binciken NDDC yayi Murabus bayan zarginshi da hannu a Badakalar ma’aikatar
Shugaban kwamitin majalisar wakilai dake binciken ma’aikatar Naija Delta, NDDC, Olubunmi, Tunji-Ojo yayi murabus daga mukamin nasa baya da aka zargeshi da hannu wajan yin cushe a kasafin kudin ma’aikatar.
Kemebradikumo Pondei wanda shine Daraktan NDDC na riko ya fice daga zauren da majalisar ke bincikenshi inda ya zargi Tunji da wasu shuwagabannin kwamitin dake bincikensa da cushe a kasafin kudin ma’aikatar na 2019.
Yace ba zai yiyu masu irin wannan laifi a ma’aikatar ya zamana kuma sune zasu binciki al’amuranta ba. Ya kuma kara da zargin cewa ma’aikatar ta baiwa Tunji kwantirakin ginin wani kamfani.
Tunji dai ya sauka daga shugabancin kwamitin inda kuma ya karyata zargin da ake masa, yace duk me shaidar ya zo ya nuna
Ajiye ra,ayinka dan gane da labaranmu sshawara ko korafi

No comments:
Post a Comment