Yaron Da Kishiyoyin Mahaifiyarsa Suka Daure A Turken Awaki Na Tsawon Shekaru Biyu A Jihar Kebbi Ya Soma Samun Sauki A Asibiti - Mahanga

Barka da zuwa shafin mahanga, Mahanga shafi ne da zai dinga kawo muku labari masu banmamaki da ban dariya , tare da littatafai na hausa wato ( novel's )

People Online

Breaking

ads

Sunday, 9 August 2020

Yaron Da Kishiyoyin Mahaifiyarsa Suka Daure A Turken Awaki Na Tsawon Shekaru Biyu A Jihar Kebbi Ya Soma Samun Sauki A Asibiti

 

Yaron da kishiyoyin mahaifiyar sa suka daure shi a turken awaki na tsawon shekaru biyu a jihar Kebbi yanzu haka yana samun sauki a asibitin Sir Yahaya dake Birnin Kebbi a jihar Kebbi.

Yanzu haka dai shugaban asibitin Sir Yahaya dake Birnin Kebbi ya taimaka masa da tufafin sakawa, abinci da magunguna.


Inda wata kungiya mai suna ZakiGems suka taimaka masa da omo na wanki, kayan abinci da takalmi

Jibril yaro ne mai dadin mu'amala. Kuma yanzu haka har ya saba da É—an sandan da yake kula da shi.

A ganin yanayin da yaron yake na fama da matsananciyar yunwa a tare da shi, yanzu haka yana cikin farin ciki bayan da aka samar masa da abinci

Yanzu haka dai Mahaifinsa da sauran kishiyoyin mahaifiyarsa da suka yi masa wannan mummunan aikin suna hannun hukumar 'yan sanda a tsare.

1 comment:

ads1