Budurwa ta kashe Saurayinta, Auwal Sulaiman saboda zargin cin Amana
Wata Budurwa, Precious Okogbua dake zaman dadaro da Saurayinta, Auwal Sulaiman ta kashe shi saboda zargin cin Amana.
Lamarin ya farune a yankin Liverpool dake Apapa, jihar Legas. Me magana da yawun ‘yansandan jihar, Bala Elkana ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama wanda ake zargi kuma an tura kes din nata bangaren binciken manyan laifuka.
Auwal me shekaru 25 sun fara sa’in’sa da farkarsa ne yayin da zargin cin amana ya bullo, kawai sai ta dauko wuka ta daba masa a wuya.
An garzaya dashi Asibitin Apapa inda aka tabbatar da cewa ya mutu.
No comments:
Post a Comment