Ma'aikatan N-power Na Zanga Zanga Yanzu Haka A Birnin Tarayya Abuja - Mahanga

Barka da zuwa shafin mahanga, Mahanga shafi ne da zai dinga kawo muku labari masu banmamaki da ban dariya , tare da littatafai na hausa wato ( novel's )

People Online

Breaking

ads

Thursday, 23 July 2020

Ma'aikatan N-power Na Zanga Zanga Yanzu Haka A Birnin Tarayya Abuja

Ma'aikatan N-power Na Zanga Zanga Yanzu Haka A Birnin Tarayya Abuja



.

Ma'aikatan N-power Na zanga zanga yanzu haka a birnin tarayyar najeriya Wato Abuja.
Zanga Zangar ta samo asali ne saboda yunkurin da gwamnatin Nijeriya keyi na sauke ma'aikatan.
Sannan akwai wasu daga cikin ma'aikatan da suka bayyana cewa an dafe musu Albashin wata 4, Kuma har yanzu Sunji shiru.
Sai dai a ta bakin Minista Sadiya Umar Faruk a wata zantawa da tashar talabijin ta NTA ta bayyana cewa tana sane dasu.
Amma duk da haka ma'aikatan sun bayyana cewa Ministar ta dade tana musu yawo da hankali kan bashin da suke binta, in har suke ganin wannan yunkuri ne na dafe musu Albashin gaba daya.
Sanadiyar wadannan matsaloli ma'aikatan sunsha shirya zanga zanga sai dai ana ganin zanga Zangar yau ta dauki Sabon salo saboda sun nuffi Zauren Majalisa.
A wata takarda da ma'aikatan suka nuna, sun bayyana cewa sunada ilimi, suna kwarewa, sun sami horonda ya kamata saboda haka sun kawo sauyi sosai a bangaren ilimi, lafiya, dakuma aikin noma.
Akwai yuyuwar masu zanga zangar a yau zasu mika korafinsu zuwa shugaban Majalisa Ahmad Lawan.
An samu mahalartar zanga zangar daga sassa daban daban na. Najeriya musamman daga birnin legas, dakuma birnin tarayya Abuja.

No comments:

Post a Comment

ads1