Wani Karin Haske Game Da Dibar Sabbin Ma'aikatan Shirin N-POWER BATCH C 2020
Muna samun tambayoyi game da shin me shaidar kwalin SSCE zai iya cikewa?
Ga yadda tsarin N-power yake :
1- N-power Agro
2- N-power Tax
3- N-power Build
4- N-power Health
5- N-power Teach
1- N-power Agro:
1- N-power Agro:
Wannan tsarin ana bukatar masu shaidar kwalin Diploma, HND da Degree, kuma wanda suka karanci fandin Agric ko Nutrition.
2- N-power Tax
Wannan tsarin suna bukatar masu shaidar kwalin HND da Degree ne kaÉ—ai, Kuma wanda suka karanci fannin Finance, Economic, ko Accounting.
3- N-power Build
Wannan tsarin suna buƙatar masu shaidar karatun SSCE, Diploma, HND da Degree, bugu da kari wanda bashi da takardan shaidar karatu ma zai iya cikewa.
4- N-power Health
Wannan tsarin suna bukatar masu shaidar kwalin Certificate, Diploma, HND da Degree.
Daga cikin wadanda suke bukata akwai:
- Midwives
- Nursing
- Medical Record
- CHO, CHEW, JCHEW
- PHARMACY
- Biology
- Biochemistry
- Health education
- EHO, EVT, EHA
5- N-power Teach
Wannan tsarin suna bukatar masu kwalin NCE, Diploma, HND, da degree.
Kada ku manta ranan Juma'a(26/6/2020) mai zuwa za'a bude wannan Portal din Kuma portal address nasu bai canza ba, wanda
akai amfani da shi na baya shi za'ayi amfani (portal.npower.gov.ng)
Allah Ubangiji Ya bawa kowa sa'a.
Daga Mutawakkil Gambo Doko
Thursday, 25 June 2020
Abin da mai npower ya kamata ya sani kamin yayi apply
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
ads1
Author Details
new platform in northern arewa
Thank u so much
ReplyDeleteTnxs
ReplyDelete