KOTU TA TABBAR DA HUKUNCIN YIN DANDAKA GA MASU FYADE - Mahanga

Barka da zuwa shafin mahanga, Mahanga shafi ne da zai dinga kawo muku labari masu banmamaki da ban dariya , tare da littatafai na hausa wato ( novel's )

People Online

Breaking

ads

Thursday, 9 July 2020

KOTU TA TABBAR DA HUKUNCIN YIN DANDAKA GA MASU FYADE

GANI GA WANE... Kotu A Kasar Somalia Ta Fara Yanke Hukuncin Yanke Al'aura Ga Masu Fyaɗe Daga Haidar H Hasheem Kano A safiyar jiya Laraba wata kotu dake kasar Somalia ta fara zartar da hukunci ga masu aikata fyaɗe ga mata. Alaƙalin ya ce wannan matakin da ya ɗauka ya yi hakan ne domin ya zama izina ga masu tunanin aikata irin wannan mummunan laifin na rashin imani. Wata jarida dake ƙasar ta wallafa labarin a Twitter biyo bayan zartar da hukuncin. Alƙalin ya yankewa matasan guda biyu hukuncin yanke al'aurar su ta hanyar dandatsa, an kama matasan biyu ne da laifin yi wa yarinya ƙarama fyaɗe a ƙasar. Shin masu karatu kuna goyan bayan irin wannan Matakin da Alƙalin ya ɗauka?

No comments:

Post a Comment

ads1